Putin da Trump sun bayyana aniyarsu ta kawo karshen rashin jituwa da warware batun Ukraine

An kammala taron tattaunawa tsakanin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka Donald Trump a birnin Alaska na kasar Amurka, inda bangarorin biyu

An kammala taron tattaunawa tsakanin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka Donald Trump a birnin Alaska na kasar Amurka, inda bangarorin biyu suka bayyana taron a matsayin mai matukar amfani.

Fadar Kremlin ta tabbatar da cewa tattaunawar ta yi armashi, yayin da manzon musamman na Rasha Kirill Dmitriev ya bayyana cewa yanayin taron ya yi kyau.

Putin ya jaddada aniyar kasashen biyu na kawo karshen kiyayyar da suke yi da kuma bukatar cimma matsaya domin kawo karshen yakin Ukraine. Ya yaba da yadda Trump ya fahimci muradun Rasha da kuma burinsa na fahimtar ainihin rikicin.

A nasa bangaren, Trump ya tabbatar da cewa tattaunawar ta kai ga cimma matsaya a kan batutuwa da dama, yayin da wasu manyan batutuwa suka rage. Ya yi nuni da cewa, zai ci gaba da tattaunawa da sauran bangarorin, ya kuma yi tsokaci da cewa a ganawarsu ta gaba za ta kasance a birnin Moscow.

A jiya ne aka fara taron koli tsakanin shugabannin biyu a filin tashi da saukar jiragen sama na Alaska tare da tattaunawa a cikin motar shugaban na Amurka.

Trump ya shaida wa Fox News cewa yana son ganin an tsagaita bude wuta a Ukraine kuma ba zai ji dadi ba idan hakan bai faru a yau ba. Ya kara da cewa Turawa ba sa gaya mani abin da zan yi, ni ke daukar shawarar abin da zan da kaina.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted