Wani jami’in sojan HKI ya yi furcu a karon farko cewa, martanin Iran ya shafi cibiyoyinta na soja.
A yau Talata ne jami’in sojan na HKI ta yi furuci irinsa na farko cewa martanin da Iran ta mayar a watan da ya shude, ya shafi sansanonin soja.
Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ne ya ambato jami’in sojan na ‘yan sahayoniya yana yin wannan furucin bisa sharadin kar a ambaci sunansa.
Harin wuce gona da iri na HKI a ranar 13 ga watan Yuli ya shafi kwamandojin soja da masana fasahar Nukiliya.
Martanin jamhuriyar musulunci na Iran akan kallafaffen yakin HKI ya shafi cibiyoyin soja, leken asiri, wuraren binciken masu alaka da soja.
Iran ta yi amfani da jiragen yaki marasa matuki da kuma makamai masu linzami mabanbanta wajen kai wa HKI hari.
HKI ce ta bukaci a tsagaita wutar yaki ta hanyar Amurka, wacce ita kuma ta tuntubi kasashe masu shiga Tsakani.
An yi kirdadon cewa, asarar da HKI ta yi, ta kai ta Dala biliyan 5.