Rasha Ta Jaddada Aniyarta Ta Karfafa Hadin Gwiwa Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Kasarsa na da niyyar karfafa hadin gwiwa da Iran da kuma kara karfin tsaron kasar ta

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Kasarsa na da niyyar karfafa hadin gwiwa da Iran da kuma kara karfin tsaron kasar ta Iran

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Riyabkov ya jaddada cewa: Kasar Rasha za ta karfafa hadin gwiwa da Iran a dukkan fannoni, gami da kara karfin tsaron kasar ta Iran.

Riyabkov ya shaidawa manema labarai a ofishin jakadancin Iran da ke birnin Moscow cewa: “Za su karfafa hadin gwiwa a aikace tare da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a dukkan fannoni, yana mai jaddada cewa: Dole ne a karfafa karfin tsaron kasar Iran, saboda Rasha tana da gogewa mai kima a wannan fanni, kuma za ta ci gaba a kan hakan.”

A ofishin jakadancin Iran, Riyabkov ya kuma sanya hannu a littafin ta’aziyya ga shahidan Iran da aka kashe a harin wuce gona da iri na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.

Wani abin lura a nan shi ne cewa: A ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata ne yahudawan sahayoniyya suka ci gaba da kai hare-hare kan yankunan birnin Tehran da wasu garuruwa da dama da suka hada da cibiyoyin nukiliya, cibiyoyin kiwon lafiya, asibitoci da kuma wuraren zama a fadin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted