Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Ce; Dokar Majalisar Shawarar Musulunci Ta Kasar Kan Hukumar IAEA Dole Ne Aiki Da Ita

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa: Dokar Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar ta dakatar da hadin gwiwa da hukumar IAEA dole ne aiki da

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa: Dokar Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar ta dakatar da hadin gwiwa da hukumar IAEA dole ne aiki da ita

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Ismail Baqa’i ya bayyana a wani taron manema labarai cewa: Dole ne hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta yi aiki nesa da batun siyasa, yana mai nuni da cewa: Dokar Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran kan dakatar da hadin gwiwa tsakanin Iran da hukumar ta IAEA, dole ne yin aiki da ita. Ya ce wannan doka ta tana nuna damuwa da fushin al’ummar Iran ne dangane da hare-haren wuce gona da iri da aka kaiwa cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran da kuma kisan gillar da aka yi wa masana kimiyyar nukiliyar kasar.

A zaman taron manema labaransa na mako-mako kan taron tunawa da juyayin shahadan Imam Husaini (a.s), Baqa’i ya ce: “A gare su makokin Ashura ba wai kawai zaman makoki ne na wani lamari mai raɗaɗi ba, a’a, abin tunawa ne na al’adu da wayewar al’ummar Iran na rayuwa ta mutuntaka.” Wato kiyaye mutuncin dan’adam, da rashin yarda da mulkin kama karya ta kowace fuska.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted