Birnin Los Angeles Na Amurka Ya Rikice Yadda Ake Dauki Ba Dadi Tsakanin Al’ummar Jihar Da Jami’an Tsaro

Birnin Los Angeles na Amurka tana ci gaba da fuskantar tashe-tashe hankula kamar yadda zanga-zanga ta mamaye birnin An ayyana dokar ta-baci a birnin Los

Birnin Los Angeles na Amurka tana ci gaba da fuskantar tashe-tashe hankula kamar yadda zanga-zanga ta mamaye birnin

An ayyana dokar ta-baci a birnin Los Angeles na Amurka yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin masu zanga-zanga da ‘yan sanda kan batun gwamnatin kasar kan batun neman murkushe bakin haure. Gwamnan California Gavin Newsom ya zargi shugaba Donald Trump da rura wutar zanga-zangar.

Gavin Newsom ya dauki Trump a matsayin wani mai karya kundin tsarin mulki ta hanyar korar bakin haure da yawa ba tare da nuna bambanci ba, yana mai bayyana tura dakarun Marines da na National Guard a matsayin wani kara ruruta water tashin hankali na rashin hankali da zai kara tada zaune tsaye a birnin.

Bayan Donald Trump ya bayyana bakin haure a matsayin dabbobi da ke dauke da tutocin wasu kasashe, Trump ya yi alkawarin cewa ba zai kyale abin da ya kira ‘yan mamaya da bakin haure daga kasashe masu tasowa na duniya su mamaye birnin California ba kuma zai bankado masu ba da tallafi ga masu zanga-zangar a California.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted