Saudiya Ta Yi Amfani Da Fasahar AI Don Sauwaka Ayukan Hajjin Shekara ta 2025

Gwamnatin kasar Saudiya ta yi amfani da fasahar kirkirarren tunani ko (AI) don sauwakawa kanta da kuma mahajjata a hajjin wannan shekara ta 2025, kama

Gwamnatin kasar Saudiya ta yi amfani da fasahar kirkirarren tunani ko (AI) don sauwakawa kanta da kuma mahajjata a hajjin wannan shekara ta 2025, kama daga kula da cinkoson mutane, kiyaye lafiyar mahajjata da haka kuma ta kyautata ayyukan mahajjata a cikin nutsuwa da rashin damuwa.

Jaridar ArabNews ta kasar Saudiya ta bayyana cewa tare da wannan fasahar ta kula da zafin dukkan wuraren da mahajjata zuwa zuwa da kuma hana cinkoson mutane a kewayen Kaaba da sauran wurare..

Jami’I mai kula da bangaren kirkirerren fasaha wato AI na aikin Ajjin bana ya shaidawa Jaridar ArabNews kan cewa sun kirkiro abubuwa da dama don sawwaka aikin hajji ga mahajjata da kuma khidimomin da kasar saudiyya take yiwa mahajjata, Ya ce an yi amfani da wannan fasahar a masallacin Madina da kuma na dakin nKaaba.

Ya ce jami’an shige da fice na kasar Saudiya suna amfani da kayakin aiki na zama a ayyukansu . sannan suna aikin bincike da kansu a tashoshin jiragen sa 11 a kasashen 7 a duniya, inda suke tabbatar da cewa mahajjaci ya cancanci ya je aikin hajji tun daga kasarsu kafin ya shiga jirgi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted