Falasdinawa 23 Suka Yi Shahada A Farmakin Da Sojojin Mamayar Isra’ila Suka Kai Kan Sansanin Al-Bureij

Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Bureij da ke kudancin Zirin Gaza

Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Bureij da ke kudancin Zirin Gaza

Falasdinawa fararen hula 23 ne suka shahada tare da jikkata wani adadi masu yawa a wani sabon kisan kiyashi da sojojin gwamnatin mamayar Isra’ila suka yi a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Bureij da ke kudancin zirin Gaza. Rahotonni sun bayyana cewa: sojojin mamayar sun kai hare-hare ne ta hanyar jiragen saman kan gidajen jama’a, ciki har da gidan iyalan Al-Qarnawi da ke gabashin sansanin.

Haka hare-haren sun yi sanadiyyar shahadar wani Bafalasdine a yankin Qizan al-Najjar da ke kudancin Khan Yunus. Sannan jami’an ceto sun gano gawar wani Bafalasdine a wani gidan da aka jefa bam a Abasan al-Kabira da ke gabashin birnin.

Bugu da kari, gobarar da jiragen saman sojojin mamayar Isra’ila suka tayar a kan yankunan Falasdinawa ta janyo shahadan wani Bafalasdine a kusa da wata cibiyar agaji a yankin da ake kira “Morag axis,” kudu maso yammacin Khan Yunis.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted