Yakin Gaza : Tarayyar Turai za ta sake nazari kan Yarjejeniyarta da Isra’ila

Bayan sabon farmakin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, kasashen Yamma na kokarin kara matsin lamba kan Isra’ila, wacce ta kauda kai kan kiraye

Bayan sabon farmakin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, kasashen Yamma na kokarin kara matsin lamba kan Isra’ila, wacce ta kauda kai kan kiraye kirayen da duniya ke yi na ta dakatar da yakin a Gaza.

Kungiyar ta EU, ta kara mastin lamba ta hanyar sake nazari kan yarjejeniyarta da Isra’ila ta tsawon shekaru 25 dake a tsakaninsu.

Tunda farko dama kasashen kasashen Canada-Faransa da Ingila  sun sanar da yin Allah wadai da farmakin kasa na soja na sojojin Isra’ila a Gaza.

Baya ga hakan kuma Birtaniyya a ranar Talata ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci da Isra’ila.

Ita ma kiasar Sweden, ta yi kira da a kakaba takunkumi ga membobin gwamnatin Isra’ila.

Bayanai sun ce yanzu haka matakan da wasu kasashen yamma ke doka , ya hadassa sabani tsakanin kasashe 27 na Tarayyar Turai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted