Trump Ya Bukaci Ukraine Ta Amince Da Tayin Putin Na Bude Tattaunawa A Birnin Istambul

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bukaci shugaban kasar Ukraine ya amince da tayin shugaban Putin na Rasah na sun hadu a birnin Istambul na

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bukaci shugaban kasar Ukraine ya amince da tayin shugaban Putin na Rasah na sun hadu a birnin Istambul na kasar Turkiya don tattauna yiyuwar  tsagaita budewa juna wuta.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto shugaban Trump yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma bayyana cewa wannan wata dama ce kawo karshen zubar da jinni tsakanin kasashen biyu na fiye da shekaru uku da suka gabata.

Trump ya bayyana haka ne a shafinsa na yanar gizo, ya kuma kara da cewa, haduwar shuwagabannin biyu zai fayyace matsayin yakin, da kuma yiyuwar dakatar da shi nan kusa. Banda haka haduwarsu zai bawa kasar Amurka damar gane matakin da zata dauka nan gaba, haka ma tarayyar turai.

Kafin haka dai a ranar Asabar da ta gabata ce, shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha ya bayyana cewwa, Rasha a shirye take ta bude tattaunawa gaba da gaba da kasar Ukraune a birnin Istambul na kasar Turkiyya a ranar 15 ga watan mayun da muke ciki wato ranar Alhamis mai zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted