Hare-Haren ‘Yan Sahayoniyya Kan Lebanon Sun Kashe Tare Jikkata Mutane 74 A Birnin Beirut

Hare-haren da jiragen saman yakin gwamnatin ‘yan sahayoniyya suka kai kan birnin Beirut da kewaye sun yi sanadiyyar mutuwa da jikkatan mutane 74 Rahotonni sun

Hare-haren da jiragen saman yakin gwamnatin ‘yan sahayoniyya suka kai kan birnin Beirut da kewaye sun yi sanadiyyar mutuwa da jikkatan mutane 74

Rahotonni sun bayyana cewa: Wasu munanan fashe-fashe sun afku a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon a safiyar yau Asabar, biyo bayan wani kazamin harin makami mai linzami da sojojin gwamnatin ‘yan sahayoniyya suka kai wanda ya yi sanadiyar tarwatsa wani bene mai hawa 8, tare da janyo shahadan mutane 11 da jikkatan wasu 63 na daban.

Hukumar kafafen yada labarai ta kasar Lebanon ta bayyana cewa: Birnin Beirut ya farka da wani mummunan kisan kiyashi, yayin da jirgin saman yakin gwamnatin mamaya ta ‘yan sahayoniyya ya kai hari da makami mai linzami 5 a wani ginin mazauni, wanda ya kunshi benaye 8, a kan titin Al-Mamoun a yankin Basta, a tsakiyar babban birnin kasar, inda ya janyo tarwatsewar ginin da lalacewan gine-ginen da ke kewaye.

Hukumar ta bayar da rahoton cewa: Masu aikin ceto na aikin kwashe baraguzan da ke kan titin Al-Mamoun a garin Basta, kuma hukumar tsaron farar hula ta Lebanon ta ce mutane 11 ne suka yi shahada yayin da wasu 63 suka jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments