Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Matakin da Turai ke son dauka kan kasarsa ya saba wa ainihin tsarin haɗin gwiwa da hukumar IAEA
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Iran tana da niyyar gudanar da hadin gwiwa da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya da kuma warware matsalolin da suka rage kan batun shirinta na makamashin nukiliya, amma matakin da kasashen Turai suke dauka kanta sun saba wa wannan kyakkyawar aniya ta kasar Iran.
A hirarsa da gidan talabijin na Al-Mayadeen Abbas Araqchi ya yi gargadi kan daukan matakin matsin lamba kan Iran, yana mai cewa, ba zai haifar da da mai ido ba, kuma ba zai hana Iran ci gaba da aniyarta ta bada hadin kai ga hukumar ta IAEA ba, yana mai jaddada cewa: Iran tana da niyyar ba da hadin kai ga hukumar ta IAEA, domin warware manyan matsalolin da ake takaddama a kai, amma matakin kasashen Turai ya saba wa wannan kyakkyawar aniya ta Iran.
Araqchi ya bayyana kokarin da Iran take yi na neman samun fahimtar juna don warware takaddamar da ke faruwa, inda ya ce:Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya, Rafael Grossi, yana da kyakkyawan fata kuma yana maraba da wannan hubbasa na Iran.
Kamar yadda Araqchi ya bayyana cewa: Manufar gayyatar Grossi zuwa Iran ita ce bude wani sabon shafi na hadin gwiwa tsakanin Iran da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya, yana mai cewa ziyarar ta kasance ta siyasa ce.