Jagoran Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen Ya Ce Sun Tilastawa Amurka Janye Jirgin Ruwanta Daga Tekun Larabawa

Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ya bayyana cewa: Sun kalubalanci Amurka da jiragen yakinta lamarin da ya tilasta mata  tserewa daga tekun Larabawa. Jagoran

Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ya bayyana cewa: Sun kalubalanci Amurka da jiragen yakinta lamarin da ya tilasta mata  tserewa daga tekun Larabawa.

Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen, Sayyid Abdul-Malik Al-Houthi a jiya Alhamis ya jaddada cewa: Al’ummar Yemen sun kalubalanci Amurka da jiragen yakinta da kuma babban jirgin ruwan dakon jiragen yakinta a cikin teku, bayan da suka shelanta kai farmaki kan su da tsayin daka, kuma al’ummar Yemen ba zasu ta taba ja da baya daga matsayinsu ba, kuma za su ci gaba da yakin “Alkawarin Neman Nasara” da gwagwarmaya Tsarkakekkiya.”

Sayyid Al-Houthi ya bayyana cewa: A yanzu jirgin ruwan dakon jiragen sama na Abraham Lincoln ya tsere daga tekun Larabawa bayan sanarwar za a kai masa hari. Ya kara da cewa: Jirgin ruwan “Abraham Lincoln” ya ji tsoron ci gaba da kasancewa a cikin tekun Larabawa kuma dama shawara ita ce ya koma inda ya fito.

Al-Houthi ya kuma jaddada cewa: Dakarun kasar Yemen za su ci gaba da gudanar da ayyukansu a teku da nufin hana zirga-zirgar jiragen haramtacciyar kasar Isra’ila a tekun Bahar Rum, Bab al-Mandab, da Tekun Larabawa har zuwa tekun Indiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments