An yi ta harbe-harbe a kusa da filin jirgin saman birnin Juba fadar mulkin kasar Sudan ta Kudu a yammacin jiya Alhamis
Kafofin watsa labaran cikin gida a Sudan ta Kudu sun watsa rahoton cewa: An ji karar harbe-harbe a kusa da filin jirgin sama na birnin Juba fadar mulkin kasar a yammacin jiya Alhamis, kuma sun watsa labarin cewa: An yi yunkurin cafke tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar, Akol Korek, wanda aka kora a watan Oktoban da ya gabata.
An fara harbe-harbe ne da misalin karfe bakwai na yamma a kusa da filin jirgin saman Juba kuma an ci gaba da harbe-harben na kusan sa’a guda, a cewar kamfanin dillancin labaran Faransa.
Yayin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa: An ji karar harbe-harbe mai tsanani a birnin Juba da yammacin jiya Alhamis a kusa da wani sansanin soji. Sannan an nakalto daga kakakin rundunar sojin kasar na cewa, yana bakin kokarinsa domin tabbatar da abin da ke faruwa a kasar.
Bangarorin da ke adawa da shugaba Salva Kiir Mayardit da mataimakinsa na farko Riek Machar sun gwabza yakin basasa daga shekara ta 2013 zuwa 2018 wanda ya yi sanadin mutuwar dubban daruruwan mutane.