Mafi yawan Yahudawan sahyuniya na goyon bayan cimma yarjejeniya da kungiyar Hamas

A wani bincike da gidan talabijin na Channel 12 na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya gudanar  ya nuna cewa, galibin yahudawan sahyuniya da aka ji

A wani bincike da gidan talabijin na Channel 12 na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya gudanar  ya nuna cewa, galibin yahudawan sahyuniya da aka ji ra’ayinsu daga ciki har da Naftali Bennett tsohon ministan gwamnatin yahudawan, suna goyon bayan yin musayar fursunoni da Hamas.

A cewar jaridar Arab 48, sakamakon binciken tashar 12 ta gwamnatin sahyoniyawa ya nuna cewa dogon lokacin da aka dauka ana yakin ya sanya ‘yan sahayoniya neman wasu muhimman abubuwa.

Bisa binciken da wannan tasha ta gudanar, kashi 69 cikin 100 na yahudawan sahyoniyawan sun yi imanin cewa, babban burin da ake da shi a wannan lokaci shi ne cimma yarjejeniya kan musayar fursunonin Isra’ila da aka kama a Gaza. Yayin da sauran kashi 20% suka yi imanin cewa ci gaba da yakin Gaza shi ne manufa mafi muhimmanci.

Amma idan aka zo kwatanta Netanyahu da Naftali Bennett, tsohon firaministan gwamnatin Sahayoniya, Bennett ya samu nasarar samun kashi 37% na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu, yayin da kashi 35% ne kawai ke kallon Netanyahu a matsayin zabi mafi kyau ga wannan matsayi na Firayim Minista.

Saboda gazawarsa wajen fuskantar turjiya daga ‘yan gwagwarmaya, da kuma aikata munanan laifuka a Gaza da Labanon, Netanyahu yana fuskantar zanga-zangar yahudawan sahyoniya a bangare guda, a daya bangaren kuma yana fuskantar Allah wadai da kotun kasa da kasa kan aikata laifukan yaki a Gaza da Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments