Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran ya jaddada cewa: Babu wani karfi da zai iya fuskantar gwagwarmaya
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Manjo Janar Hossein Salami ya jaddada cewa: Babu wani karfi komai karfinsa da zai iya fuskantar gwagwarmaya ya zauna lafiya.
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Hossein Salami ya bayyana haka ne a yayin babban atisayen tsaron na nasarar Allah da aka gudanar a birnin Tehran fadar mulkin Iran yana mai jaddada cewa: Mayakan Musulunci suna bayyana baje kolin wani yanayi mai ban mamaki na hadin kai da karfi da fahimtar juna, kuma matukar wadannan dakaru da ba su da iyaka suka lashi takwabin kare Musulunci da maslahar kasa da al’ummar musulmi, babu wani karfi kuma komai jin kansa ko Amurka ce da kasashen Turai da suke kawance da juna tare da tallafin karamar alhaki gwamnatin ‘yan sahayoniyya da za su iya kalubalantar Dakaru masu imani da ruhin gwagwarmaya da akidar shahada.
Janar Salami ya kara da cewa: Arangamar da ake yi tsakanin Falasdinu, Lebanon, Iran, Yemen, Iraki da sauran yankunan duniyar musulmi a halin yanzu wajen tunkarar rundunar mushrikai da ‘yan sahayoniyya abin kyama da kawayensu da mabiyansu na yammaci, karo ne na hakika, mai tarihi da zai wanzu a kyakkyawan kundin na musamman da zai dawwama da sunan Musulunci da imani da kare mutuncin kasa a gaban wadannan makiya.