Rundunar sojin mamayar Isra’ila ta yi furuci da halakar sojojinta masu yawa a kudancin kasar Lebanon
Rundunar sojin mamayar yahudawan sahayoniyya ya yi furuci da cewa: Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasat Isra’ila biyar ne suka sheka lahira, yayin da wasu 16 nadaban suka jikkata a fadace-fadacen da aka gwabza tsakanin sojojin ‘yan sahayoniyya da ‘yan kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi a yankin kudancin kasar Lebanon a cikin ‘yan kwanakin nan da suka gabata.
Shafin yanar gizo na sojojin mamayar Isra’ila a jiya Alhamis ya bayyana cewa: A cikin sa’o’i 24 da suka gabata an jikkata sojoji 10, 8 daga cikinsu a yakin kasar Lebanon, 2 a Zirin Gaza, yayin da sojoji 21 suka jikkata a yakin da ake gwabzawa da ‘yan gwagwarmaya a bangarorin biyu a jiya.
A cewar shafin yanar gizon, adadin wadanda suka jikkata a Gaza, da gabar yammacin kogin Jordan da Lebanon ya kai sojoji 5,292 tun farkon yakin kisan kare dangi a Gaza a ranar 7 ga Oktoban shekara ta 2023.