Iran Ta Yi Kiran A Kara Kaimi Wajen Samar Da Zaman Lafiya A Gaza Da Lebanon

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta yi kiran da a kara kaimi wajen samar da zaman lafiya a Gaza da Lebanon. Wannan kiran ya fito ne

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta yi kiran da a kara kaimi wajen samar da zaman lafiya a Gaza da Lebanon.

Wannan kiran ya fito ne ta bakin ministan harkokin wajen kasar Abass Araghchi a wata tattaunawa ta wayar tarho tare da takwaransa na Masar, Badr Abdelatty a yau Litinin.

Mista Araghchi ya yi kira da a fadada yunkurin diflomasiyya don samar da zaman lafiya a Gaza da Lebanon, inda ya jaddada muhimmancin tsagaita bude wuta a yankunan da aka mamaye.

Ya yi kira da a gaggauta kai kayan agaji ga ‘yan gudun hijira a Gaza da Lebanon.

Araghchi ya ce shugabannin Isra’ila na da burin fadada yakin a duk fadin yammacin Asiya.

Ya ce yahudawan sahyoniya suna son kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Iran na bayan tsagaita bude wuta amma tana da hakki nata na kare kanta daga duk wani hari na Isra’ila, in ji shi.

Ministan na Iran ya jaddada bukatar daukar kwararan matakai a duk fadin duniya, musamman ma al’ummar musulmi, don dakile abinda ya danganta da na’urar kisan kare dangi ta Isra’ila.

Shi ma a nasa bangare minsitan harkokin wajen kasar ta Masar Abdelatty, ya fifiko yunkurin warware rikicin yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments