Zaben Amurka : Aski Ya Iso Gaban Goshi

A Amurka za’a iya cewa ‘yan sa’o’I ne suak rage al’ummar kasar su je ga kada kuria’a a babban zaben kasar. Za’a fafata a zaben

A Amurka za’a iya cewa ‘yan sa’o’I ne suak rage al’ummar kasar su je ga kada kuria’a a babban zaben kasar.

Za’a fafata a zaben mafi daukan hankali a tsakanin ‘yar takara magajiyar Joe Biden kana kuma mataimakiyarsa Kamala Harris daga jam’iyyar Demokrate da kuma tsohon shugaban kasar Donald Trump daga jam’iyyar Republican.

 ‘Yar takarar ta jam’iyyar Demcorat Kamala Harris za ta shafe yinin ranar Litinin a jihar Pennsylvania, sannan ta kammala da taro a Philadelphia.

Donald Trump a nasa bangaren, ya shirya taruka guda hudu a jihohi uku, inda zai fara da Raleigh a jihar North Carolina, sannan ya yada zango sau biyu a Pennsylvania, ya kuma gudanar da wani taro a Reading da Pittsburgh.

Idan har Trump, ya lashe zaben zai zama shugaban Amurka na biyu a tarihin kasar da ya lashe zaben shugaban kasa ba a jere ba, bayan Grover Cleveland a karshen karni na 19.

Ita kuwa ‘yar takara Harris tana neman zama mace ta farko, kuma Ba’amurkiyar Afirka ta farko kuma mutum na farko mai asalin jinin Asiya ta kudu da za ta kai ga Ofishin Shugaban Kasa, shekaru hudu bayan ta ta farko a matsayin mataimakiyar shugaban kasa.

Tuni dai Amurkawa kimanin miliyan 77 sun riga sun kada kuri’a tun da wuri, amma Harris da Trump suna kokarin jawo karin miliyoyin magoya baya su fito a zaben na gobe Talata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments