Turkiyya ta fara wani shiri na kara wayar da kan duniya kan dakatar da sayar da makamai da harsasai ga gwamnatin Isra’ila tare da aikewa da wata wasika ga kwamitin sulhun tare da goyon bayan kasashe mambobin MDD 52 da kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya 22.
Kasashen da suka rattaba hannu kan wasikar sun bukaci duniya da ta daina aika alburusai da makamai zuwa Isra’ila tare da neman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki matakai kan hakan.
An aike da wasikar ne a ranar 1 ga watan Nuwamba zuwa ga Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, da kungiyar hadin kan musulmi da kasashe 52 da suka hada da Turkiyya, Iran, Falestine, Bahrain, Bangladesh, UAE duk suna cikin kasashen da suka bukaci hakan.
Sauren sun hada da Bolivia, Brazil, Brunei, Burkina Faso, Aljeriya, Djibouti, China, Indonesia, Morocco, Gambia.
A daya bangaren kuma akwai kasashen da suka hada da Afirka ta Kudu, Irak, Qatar, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Colombia, Comoros, Kuwait, Cuba, Libya, Lebanon, Maldives, Malaysia, Mexico, Egypt, Mauritania, Namibia, Nigeria, Nicaragua, Norway, Pakistan, Russia, Saint Vincent da kuma Grenadines, Sao Tome and Principe, Senegal, Somalia, Sudan, Saudiyya Arabia, Chile, Tunisia, Oman, Jordan, Venezuela, Vietnam, Yemen, da Zimbabwe.