Bayanai daga Falasdinu na cewa fiye da mutane 1,800 ne sukayi shahada a yayin da wasu daruruwa suka bace tun bayan da Isra’ila ta kaddamar da wani sabon kisan kare dangi a arewacin Gaza a watan jiya, kamar yadda hukumomin yankin suka sanar.
A cikin wata sanarwa da aka fitar yau Litinin, ofishin yada labaran gwamnatin Gaza ya ce an kashe mutane 1,800 tare da jikkata 4,000 a arewacin Gaza a cikin watan Oktoban da ya gabata.
Tun daga ranar 6 ga watan Oktoba ne sojojin Isra’ila suke kai farmaki ta kasa a arewacin Gaza musamman a kusa da yankin Jabalia.
Sojojin mamaya sun kuma hana duk wasu motocin daukar marasa lafiya ko ayarin motocin agaji shiga arewacin Gazar.
Kawo yanzu dai adadin falasdinawan 43,374 ne sai kuma wasu 102,261 suka jikkata a hare-haren da sojojin Isra’ila ke ci gaba da kai wa a Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, in ji ma’aikatar lafiya ta yankin.
Ma’aikatar ta kara da cewa, daga cikin wadannan Falasdinawa 33 ne aka kashe sannan 156 suka jikkata a cikin sa’o’i 24 na baya-bayan nan.