Dakarun Izzuddeen Al-Qassam Ta Dauki Alhakin Halaka Babban Jami’i Da Kananan Sojojin Isra’ila A Jabaliya

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam sun dauki alhakin kashe wani babban jami’in soji da wasu sojojin mamayar Isra’ila 3 a garin Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam sun dauki alhakin kashe wani babban jami’in soji da wasu sojojin mamayar Isra’ila 3 a garin Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza

Dakarun shahidan Izzuddeen Al-Qassam, bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, suna ci gaba da kai hare-hare a rana ta 393 da fara yakin “Ambaliyan Al-Aqsa”, inda suka kai farmaki kan motocin sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da suke kutsawa cikin Zirin Gaza, inda suka yi nasarar tarwatsa wasu motocin da haka ya yi sanadiyyar halakar sojoji uku tare da jikkata wasu na daban tare da hasarar kayan yaki.

A cikin fitattun ayyukan Dakarun Izzuddeen al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, sun dauki alhakin kashe wani babban jami’in sojin tare da wasu da sojoji 3, wadanda suke cikin sashin “Fatalwa” na rundunar sojin Isra’ila ko kuma “Bangaren soji ta 888”, wanda daya ne daga cikin rukunin sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na musamman, kuma rundunar sojin mamaya ta yi ikrari da kashe su a ranar 29 ga watan Oktoban da ya gabata a garin Jabaliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments