Iran Ta Yi Tofin Allah Tsine Kan Harin Da Isra’ila Ta Kai Kan Kungiyar Ba Da Agajin Ta Red Crescennt

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi Allah wadai da harin wuce gona da iri da ‘yan sahayoniyya suka kai wa asibitin Red Crescent  

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi Allah wadai da harin wuce gona da iri da ‘yan sahayoniyya suka kai wa asibitin Red Crescent  

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Bagha’e ya dauki matakin wuce gona da iri na ‘yan ta’adda yahudawan sahayoniyya kan asibitin kula da marasa lafiya na wucin gadi da kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta kafa a kan iyaka da ke tsakanin kasashen Siriya da Lebanon a matsayin laifin yaki tare da yin Allah wadai da shi da kakkausar murya gami da neman fitar da yin tofin Allah tsine da Allah wadai daga cibiyoyin kasa da kasa a fili.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Baghaei, ya jaddada yin kakkausar suka kan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kwarya-kwaryan asibitin sha ka tafi na kungiyar ba da agajin Red Crescent da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kafa a yankin kan iyaka tsakanin Siriya da Labanon, yana mai kallon hakan a matsayin tabbatar da laifukan yaki da rashin dan Adamtaka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments