Fira ministan kasar Spain Pedro Sanchez a yau Juma’a ya bukaci kasashen duniya da su daina sayar da makamai ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai yin Allah wadai da hare-haren da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kaddamar kan Dakarun kai daukin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya na “UNIFIL” da suke kudancin kasar Lebanon.
A bayan ganawarsa da PaparomaFrancis a fadar Vatican na Mabiya addinin Kirista, Sanchez ya yi kakkausar suka kan yadda hare-haren haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da janyo tabarbarewa al’amura a yankin Gabas ta Tsakiya. Fira ministan na kasar Spain ya ce: A ba shi dama a wannan mataki ya yi soka tare da yin Allah wadai da hare-haren da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan tawagar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Lebanon.
Sanchez ya yi kira ga kasashen duniya da su yi koyi da kasar Spain da ta daina sayar wa haramtacciyar kasar Isra’ila makamai tun a watan Oktoban shekara ta 2023, da nufin hana ci gaba da ruruwar wutar tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya.