Kungiyar Hizbullahi Ta Kai Munanan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta kai hare-hare kan muhimman wurare a haramtacciyar kasar Isra’ila Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi da ke

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta kai hare-hare kan muhimman wurare a haramtacciyar kasar Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi da ke kasar Lebanon daga manyan cibiyoyinta na harba makamai ta ci gaba da yin luguden makamai masulinzami da harba bama-bamai kan garuruwa da matsugunan yahudawan sahayoniyya da suke arewaci da muhimman cibiyoyin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma wuraren da aka jibge sojojin mamaya, a daidai lokacin da sojojin tsaron sararin samaniyar Isra’ila suka kasa dakile makaman Hizbullahi, don haka suke isa inda aka harba su.

A cewar kafar watsa labaran yahudawan sahayoniyya, makaman kungiyar ta Hizbullah sun fado a yankin Kiryut da ke birnin Haifa da kuma yankin masana’antu a Kiriyat Bialik a tsakanin Haifa da Akka da aka mamaye kamar yadda wasu makaman masu linzami da aka harba suka fado kan wani wurin sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila.

Sabbin kai hare-haren bama-bamai a arewacin haramtacciyar kasar Isra’ila yana zuwa ne kwana guda bayan da aka kwashe tsawon kwanaki ‘yan gwagwarmayar Hizbullahi suna yin luguden wuta kan matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida na Yaroun, Kafur Giladi, yammacin matsugunin yahudawa na Manara, Karmi’el, Beit Hillel, Kiryat Shumona, yankin Marj da Zofulon a arewacin birnin Haifa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments