Lebanon: Jiragen Yakin HKI Sun Kai Hare Hare Kan Unguwar Dahiya Junubiyya Na Birnin Beirut A Jiya Alhamsi

Jiragen yakin HKI sun yi luguden wuta a kan unguwar dahiya junubiyya na birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon, inda suka kashe mutane kimani dozun

Jiragen yakin HKI sun yi luguden wuta a kan unguwar dahiya junubiyya na birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon, inda suka kashe mutane kimani dozun biyu.

Tashar talabijin ta presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar ma’aikatar lafiya a birnin Beirut tana bayanin cewa mutane 22 ne suka yi shahada a yayinda wasu 117 suka ji rauni.

Labarin ya kara da cewa asbitoci a yankuna da dama suna jinyar wadanda suka ji rauni. Daga ciki har da asbitin jami’ar Amurka da ke Beirut inda wasu matasa suka taro don bada taimakon jini idan ana bukata.

Unguwar dahiya junubiyya na birnin Beirut dai yana daga cikin wuraren da jiragen yakin HKI suka fi kaiwa hare hare saboda nan ne matattaran magoya bayan kungiyar Jizbullah wacce take fafatawa da sojojin yahudawan fiye shekara guda.

Hizbullah ta tilastawa yahudawan a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye kimani 230,000  kauracewa matsugunansu.

A cikin yan makonnin da suka gabata ne sojojin yahudawan suka farwa kudancin Lebanon da nufin dawoda yahudawan zuwa yankunan su, amma dakarun Hizbullah sun hana hakan faruwa. Banda haka sun kara korar wasu karin yahudawan kauracewa yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments