Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Kiran Da A Hukunta Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Kasar Iran ta yi kira ga kasashen duniya da su hukunta gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan muggan laifukan da take aikatawa a kasashen Lebanon da

Kasar Iran ta yi kira ga kasashen duniya da su hukunta gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan muggan laifukan da take aikatawa a kasashen Lebanon da Falasdinu

Jakadan Iran kuma wakilinta na din din din a birnin Geneva Ali Bahraini, a cikin wata musayar takarda da aka yi tsakanin manyan cibiyoyi biyu da aka dorawa alhakin kare hakkin dan Adam da hakkokin bil’adama, ya bukaci da a dauki matakin gaggawa don hukunta gwamnatin yahudawan sahayoniyya a kan ayyukan wuce gona da iri da take aikatawa a kasashen Lebanon da Falastinu, don tilasta mata dakatar da munanan hare-haren zalunci da take kai wa.

Ali Bahraini ya aike da wasiku daban-daban guda biyu ga shugaban kungiyar agaji ta Red Cross da kuma hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, inda ya yi Allah wadai da hare-haren baya-bayan nan da yahudawan sahayoniyya suka kai a kasar Lebanon, yana mai neman mayar da martani cikin gaggawa daga kasashen duniya kan hare-hare da laifuffukan kasa da kasa da haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata tare da hukunta ta kan wadannan laifuka.

A cikin wadannan wasiku guda biyu, jakadan na Iran ya yi kakkausar suka ga harin da yahudawan sahayoniyya suka kai a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon, wanda ya kai ga shahadar Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah, da mukarrabansa, ciki har da (Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran), Birgediya Janar Abbas Nilforshan. tare da la’akari da hakan a matsayin wata alama ta take hakkin bil’Adama da kuma dokokin jin kai na kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments