Bangaren Sojin Kungiyar Hamas Ya Jinjinawa ‘Yan Gwagwarmayar Kasar Iraki

Kakakin bangaren sojin kungiyar Hamas ya albarkaci harin da ‘yan gwagwarmayar kasar Iraki suka kai kan yankin Tuddan Julan na kasar Siriya da aka mamaye

Kakakin bangaren sojin kungiyar Hamas ya albarkaci harin da ‘yan gwagwarmayar kasar Iraki suka kai kan yankin Tuddan Julan na kasar Siriya da aka mamaye

Kakakin dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, Abu Ubaida, ya albarkaci farmakin da ‘yan gwagwarmayar kasar Iraki suka kai kan sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin Tuddan Julan na kasar Siriya da aka mamaye wanda ya yi sanadin halakar sojojin yahudawa tare da jikkatan wasu na daban.

Abu Ubaida ya ce: Suna jinjina wa ‘yan uwansu ‘yan gwagwarmayar Musulunci na Iraki bisa goyon bayan da suke bai wa al’ummar Falastinu a fagen fuskantar wuce gona da irin yahudawan sahayoniya, kuma suna murna kan hari na musamman da ‘yan gwagwarmayar suka kai wa tawagar sojojin mamaya a Tuddan Julan, inda suka janyo mummunar barna tare halaka sojoji da kuma jikkata wasu na daban.

Kakakin na bangaren sojin ya kara da cewa: Farmakin baya bayan nan da jiragen saman yakin ‘yan gwagwarmayar kasar Iraki suka kai kan sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya ya yi sanadiyyar hasarar rayukan yahudawan sahayoniyya tare da isar da sako ga ‘yan mamaya cewa dagewar da su ke yi kan ayyukan zaluncinsu zai kara jawo musu hasara da koma baya, wanda hakan zai hanzarta haifar da fatattakar su daga kasashen da suka mamaye, da Yardan Allah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments