Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya bayyana cewa: Kasashen Yamma da suke bai wa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila makaman da take amfani da su wajen aiwatar da kisan kiyashi a Gaza da Lebanon, suna tarayya da ita a muggan laifukan da take aiwatarwa kan Falasdinawa da al’ummar Lebanon.
Erdogan ya jaddada cewa: Wadanda suke ba da makamai ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suna tarayya da yahudawan sahayoniyya a ci gaba da cin zarafin al’ummar Falasdinu da Lebanon.
Shugaban kasar ta Turkiyya a cikin jawabinsa ya jaddada cewa: Akwai wadanda ke jin dadin kashe yara tun suna kanana da mata, lamarin da ya zo daidai da ci gaba da goyon bayan kasashen yammacin duniya ga cibiyar kashe-kashe da aiwatar da kisan kiyashi.