Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gana da shugaban gwamnatin rikon kwarya a kasar Labanon Najib Mikati a ziyarar da ya kai birnin Beirut, ya kuma tabbatar da aniyar Tehran na goyon bayan kasar Labanon dangane da hare-haren da Isra’ila ke kai wa kasar.
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa kasarsa ta kuduri aniyar tallafawa gwamnatin kasar Lebanon da al’ummarta da kuma tsayin daka wajen tunkarar ayyukan woce gona da iri na Haramtacciyar kasar Isra’ila.
Kalaman na Araqchi sun zo ne a ziyarar aiki da yake gudanarwa a birnin Beirut, inda yake jagorantar wata babbar tawaga da ta kunshi manyan jami’ai na gwamnatin Iran.
Ministan na Iran ya ce; Tehran “za ta kaddamar da wani kamfen na diflomasiyya don tallafawa Lebanon,” inda ya bukaci taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi, ya kara da cewa munanan laifukan da Isra’ila ta aikata kan Lebanon da Palasdinawa babban misali ne na laifukan yaki.
A daidai lokacin da ya isa ofishin jakadancin Iran da ke birnin Beirut, Araqchi ya jaddada wajabcin yin amfani da dukkan karfi da kuma karfin diflomasiyya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke da shi wajen tallafa wa kasar Labanon, wajen fuskantar munanan ayyukan da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take aiwatarwa, tare da kiran kasashen musulmi da na Larabawa da su sauke nauyin da ya rataya a kansu dangane da hakan.
A nasa bangaren, Mikati ya nuna takaicinsa dangane da abin da ya bayyana a matsayin “rashin tasiri na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wajen fuskantar bala’oi masu hatsarin gaske da yahudawan sahyoniya suke haddasawa a yankin gabas ta tsakiya.