Majalisar Dokokin Libiya Ta Amince Da Nadin Sabon Gwamnan Babban Bankin Kasar

Majalisar wakilan Libiya ta amince da nadin gwamnan babban bankin kasar da mataimakinsa Majalisar wakilan Libiya ta amince da nadin Naji Muhammad Issa Belqasim a

Majalisar wakilan Libiya ta amince da nadin gwamnan babban bankin kasar da mataimakinsa

Majalisar wakilan Libiya ta amince da nadin Naji Muhammad Issa Belqasim a matsayin sabon gwamnan babban bankin kasar ta Libiya, a kokarin da ake yi na kawo karshen rikicin da ya haifar da raguwar hako albarkatun man fetur a kasar. Majalisar ta kuma amince a zamanta da aka watsa a gidan talabijin a jiya Litinin, ta nada Mar’ei Raheel Al-Bar’assi a matsayin mataimakinsa.

Yarjejeniyar za ta iya ba da gudummawa wajen shawo kan manyan matsalolin siyasa don warware rikicin da ke da nasaba da kula da babban bankin kasar ta Libiya da kuma kudaden shiga na man fetur, rikicin ya haifar da raguwar yawan albarkatun man fetur na kasar, wanda kasafin kudin kasar ya dogara a kansu sosai.

A baya dai Belqasim ya rike mukamin Darakta na Sashen Kula da Kudi da Banki a Babban Bankin Kasar, yayin da aka nada Al-Bar’assi Mataimakin Gwamna a shekara ta 2023. An nada su ne a tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya kwanan nan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments