Kissoshin Rayuwa: Sirar Fatimah (s) 45

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’aini mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da lattafin Dastane Rastan na Shahid Ayatullahi Murtdha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na Maulana Jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro za su kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra(s) diyar manzon Allah(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) da muke mawo muku, mun yi magana mai yalwa dangane  da yadda Zahra;u (s) ta sha duka a hannun wasu sabban manzon All..(s) wadanda suka shiga gidanta da nufin fitar da Aliyu dan Abitalib da karfi saboda yayi bai’a wa khalifa Abubakar.

Kuma a cikin wannan halin ne suka daketa a cikinta, suka karya awazanta suka kuma sanya ta, ta zubar da cikinta, na danta wanda ake kira Muhsinu, yana dan watanni shida a cikin mahaifiyarsa.

Sannan munji yadda sanadiyyar haka ta yi rashin lafiya wanda daga nan bata sake tashi ba har ta riski ubangijinta, tana matsayin wacce aka zalunta kuma shahidiyya.

Mun kawo maku wasu kisidun da malaman tarihi suka tsara dangane da hakan, inda suka ambaci yadda aka cutar da Zahra (s) a bayan watafin mahaifinta manzon All..(s). daga cikin kasidun akwai wacce take cewa:

Shin Ka san kirjin Fatimah da kuma Kusoshi-Ka san Halin awzarta wanda aka karya.

Menen zubar da cikin, memene jan idonta, da kuma halin yan kunnenta wanda aka  tarwatsa shi.

Wani mawakin yana cewa: Ban san labarin kuusoshi ba- Tambayi kirjinta taskar asirai.

Bayan haka sai Zahra’u (s) ta nemi taimakon koyangarta Fiddatu, ta daga murya tana cewa Ya Fiddah, ki zo ki daukeni, ki jinginani da kirjinki, wallahi sun kashe abinda ke cikin ciki na,!

Sai fiddad ta yi sauri ta zo ta dauki Fatima(s) don ta kaita daki, sai kafin ta shiga dakin cikinta ya zube. Abin sani shi ne zubar da ciki yafi haihuwa zafi, don haka Fatima (s) diyar manzon Allah(s) ta kasance tana nishin zafi.

Bayan haka tana ganin suka kama mijinta da karfi bayan da suka kwace makamin dake hannunsa suka kuma daure wuyansa da igiya suka jawo shi da karfi zuwa masallaci don yayi bai’a.

Abin mamaki, wata rana ma’awiya dan Abusufyan, a lokacinda ya yi tawaye wa Imam Ali(s) a shekara ta 37 bayan hijira an ji shi ya na aibata Imam Ali (a) da wannan, yana cewa: Ana janka kamar yadda ake jan rakumi don kayi bai’a. ..har zuwa karshen maganarsa.

Kamar yadda ya zo cikin littafin sharhin Nahjul balaga na Ibn Abilhadidi. Amma sai Imam (s) ya bashi amsa yace, kace: Ana ja na kamar yadda ake jan rakumi don inyi bai’a, na rantse da Allah kana son ka aibata sai ka yaba. Kuma kana son kunyatawa sai ka ji kunya, don ai musulmi bai da laifi idan ya kasance wanda aka zalunta. Wanda bai kasance yana shakka a adininsaba, ko kuma yana taraddudi cikin sakankancewarsa ba, wannan hujjata ce a kan waninka wanda yake nufin kwaceta daga hannun na. …har zuwa karshen zancensa.

A lokacinda ake je da Imam Ali(a) masallaci, kamar yadda Ibn Kutaiba ya kawo a cikin littafinsa {Al-Imama wassiyas}. An ce an zo da Aliyu (a) gaban Abubakar yana cewa: Ni Bawan Allah ne kuma dan’uwan manzon Allah(s). sai aka ce masa: Ka yi bai’a. Sai yace: Ni na fi cancantar bai’a a cikin wannan al-amarin. Ba zan yi maku bai’a ba, ku kuka fi cancanta ku yi mani bai’a.

Kun kwace wannan shugabanci daga Ansaru, kun hujjacesu da cewa kun fi su kusa da manzon Allah(s) da su. Amma ku kuma kun kwaceta da zalunci daga Ahlul-baitin. 

Shin baku fadawa Ansaru kan cewa ku kuka fi cancanta don matsayin ku a wajen Muhammadu(s) ba, sai suka sake maku ragamar shugabancin, suka mikata gareku? To ni ma a yanzun ina kafa hujja a kanku bisa abinda kuka hajjace Ansaru da shi.

Mu mukafi kusanci da manzon All..(s) a raye da kuma bayan wafatinsa. Ku yi mana adalci, idan kuna jin tsaron Allah

Sai Umar yace: Ba za’a taba barinka ba, sai kayi bai’a. Sai Ali (a) ya ce masa: Ka goya masa baya a yau don ya mayar maka ita gobe. Sai ya ce masa: Ya Umar ba zai amince da zancenka ba. Ba zan yi masa bai’a ba.

Sai Abubakar ya ce masa. Ba zan tilasta maka ba, idan ka ki yin bai’a. Sai Ali (a) yace:

Ya ku muhajirun!  na hadaku da Allah na hada ku da Allah kada ku yarda ku fitar da al-amarin ikon Muhammadu (s) cikin larabawa daga koryar gidansa ku maida shi zuwa koryar gidajenku, kada ku tunkude iyalan gidansa daga matsayin da Allah ya bashi a cikin mutane, kada ku kwace hakkinsa.

Na rantse da Allah  ya ku muhajirun! Wallahi mu Ahlibaiti mun fi cancanta da wannan al-amarin daga ku, saboda wadanda suke da karatun alkur’ani daga cikimmu ne, sanin masanain fikihun addini Allah daga cikimmu ne, masanan sunnonin manzon Allah daga cikimmu ne.

Sai kuma Ayyashi cikin tafirinsa ya kawo cewa: …An fitar da shi daga gidansa dabaibaye da igiyoyi, suka bi da shi ta kabarin manzon Allah(s)  sai ya ce: Ya dan mahaifiyata lalle mutane na sun kaskantani, sun kuma kusan kashe ni, sai Umar ya ce masa ka yi bi’a, sai Aliyu yace: Idan bai yi ba fa sai me? Sai Umar yace: da kuwa zan katse wuyarka. Sai Aliyu (a) yace: Da kuwa ka kashe bawan Allah wanda aka kashe kuma dan’uwan manzon Allah ne.

Sai Umar yace: Amma bawan Allah! haka ne, amma danuwan manzon Allah ba haka ba.

A cikin wata ruwaya: Amma dan’uwan manzon Allah ba zamu amince da shi ba. Sai Aliyu ya ce: Kuma musan cewa manzon Allah  (s) ya kulla yan’uwantaka tsakanina da shi ?

Sai ya ce: Ee.

Don haka an yi jayayya mai yawa tsakanin Khalifan manzon Allah(s) da kuma jama’ar da suka kwave mulki daga hannun iyalan gidan manzon All..(s). Ana cikin wannan halin sai Fatimah ta isa masallaci, tana rike da hannun yayanta Alhassan da Alhussain. Ba wata bahashimiya da tare rage sai da ta fito tare da ita. Sai Fatimah (s) ta ga mijinta baban Hassan yana tsare a hannu tare da barazanar kasheshi.

Sai ta zo tana daga murya tana cewa ku kyale dan ammi na, ku bar Aliyu. A wata ruwayar tace: Ya Ababakar kana son ka maida ni bazawara da kashe mijina. A cikin wata ruwayar tana cewa: me ya hadani da kai Ya Abubakar, kana son maida yayana marayu, sannan ka maida ni bazawara?

Daga nan sai wani mutum ya fadawa Abubakar me kakeso da wannan abinda kake? Kana son ka saukar da azaba a kan wannan al-umma ne?

Sai Aliyu (a) ya fadawa Salman cewa: Ka je ka samu yar Muhammad (s) ka bata hakuri ta dawo…

Sai salaman ya bita, sai ya ce mata ya diyar Muhammad (s) Lalle Allah ya aiko babakin rahamane ga talikai, ki koma …..har zuwa karshen maganarsa.

Sai ta ce: Ya Salman suna son  kashe Ali(s). a nan ba zan yi hakuri ba, ka barni inje kabarin babana…. Sai salman ya ce: ina jiwa mutanen Madina tsoro…  kuma Aliyu yace in fada maki cewa ki dawo. Sai tace: To zan koma zan yi hakuri zan ji zancensa kuma zan yi biyayya a gareshi.

A cikin littafin Ihtijaj Azzahra na Ridwanun Najafi sh. 140 yana cewa . Sai Aliyu(a) ya zo wajen Fatima (s) ya na gaggawa, a lokacinda ya isa wajenta sai ta na sumbantar kafadarsa tana fada masa- al-hali hawaye na kwarara daga idanunta- tana cewa: raina fansar ranka, kuma raina kariya ga ranka. Ya Baban Hassan idan ka kasance cikin alkhairi ina tare da kai, hakama idan kana cikin sharrki ina tare da kai.

Atakaice Zahra bata koma gida  ba sai da ta kubutar da mijinta daga hannun wadanda suke son tilasta masa bai’a.  suka koma  gida tare.

Masu sauraro saboda kurewar lokaci a nan zamu dasa aya sai kuma wata fitowa idan Allah ya   kaimu. Wassalamu alaikum wa rahmatullhi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments