Shahadar Sayyid Hassan Nasrallah

Shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Manar ya bayar da rahoton cewa, kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta tabbatar da shahadar Sayyid Hassan

Shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Manar ya bayar da rahoton cewa, kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta tabbatar da shahadar Sayyid Hassan Nasrallah ta hanyar fitar da sako.

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Labanon ta sanar a cikin wata sanarwa cewa: jagoran gwagwarmaya, bawa salihi, jajirtaccen shugaba mai hikima da basira mai imani da Allah madaukakin sarki, wanda ya tafi tafarkin yardarsa, ya shiga cikin madawwama ayarin shahidai.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya bi sahun shahidansa masu girma da wadanda suke tare da su tsawon shekaru kimanin 30, kuma a wannan lokaci sun kai ga nasara ta samun babban burinsu, shi ne shahada a tafarkin gaskiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments