Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, sanadiyyar hare-haren ta’addancin HKI a kasar Lebanon, adadin mutanen da su ka yi shahada sun kai 274 yayin wadanda su ka jikkata su ka kai 10,24.
HKI ta kai hare-haren ne a cikin garuruwa da kauyuka mabanbanta na kudancin Lebanon da kuma gabashinta da kuma yankin al-tuffah.
Hare-haren sun shafi garuruwan Nabadiyyah, Zahrani da Biqa’ul-Garbi. Haka nan kuma jiragen yakin HKI sun kai wasu hare-haren akan yankunan Saida, da Biqaul-Sharqi, sai Hirmil.
Motocin daukar marasa lafiya sun riga zarya akan titunan garuruwan da aka kai wa hare-haren domin daukar gawawwaki da kuma wadanda su ka jikkata.
HKI ta yi amfani da jiragen sama ne wajen kai hare-haren, haka nan kuma manyan bindigogi.
A nata gefen kungiyar Hizbullah ta sanar da kai hare-haren mayar da martani ta hanyar harba rokoki da makamai masu linzami akan sansanonin soja da kamfanonin kera makaman yaki na HKI. Garuruwan da hare-haren kungiyar ta Hizbullah ya shafa sun hada da Safad, Nahariya, Haifa da Nasirah.