Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran Muhammadu Islami ya bayyana cewa; Cigaban da Iran take samu a cikin fagage da dama yana bata ran kasashe masu danniya a duniya.
Muhammad Islami wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron tunawa da masanan Iran da su ka shahada ya ce; Juyin musulunci na Iran, ta hanyar masana da malamai, ya samu cigaba a fagage mabanbanta da hakan ne yake bakantawa makiya.
Shugaban hukumar makamashin Nukiliyar na Iran ya kara da cewa; A halin yanzu Iran tana da ilimomin da makiya ba su son wani in ba su ba, ya same su, da su ka hada da fagen hanyoyin sandarwa na zamani, da makamashin Nukiliya. Haka nan kuma ya yi ishara da yadda Iran din ta harba tauraron dan’adam dinta na farko a shearar 2008 da ya zama mabudin shiga wannan fage na fasahar sararin samaniya.