Pezeshkian: Sakonmu Na Zaman Lafiya Da Tsaro Ne Ga Dukkanin Al’ummomin Duniya

Kamfanin dilalnin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, shugaban kasar Iran Masus Pezeshkian ya ce; sakon da Iran take dauke da shi na zaman

Kamfanin dilalnin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, shugaban kasar Iran Masus Pezeshkian ya ce; sakon da Iran take dauke da shi na zaman lafiya da tsaro ne da kuma tabbatar da wannan take na  Majalisar Dinkin Duniya, wato zaman lafiya da makoma mai kyau da ci gaba ga kowa a duniya.

Maimakon zubar da jini, yaki, da kashe-kashe, dole ne mu samar da duniya da kowa zai rayu cikin jin dadi ba tare da la’akari da  launin fata, kabila, da kuma inda suka fito ba.

Shugaban na Iran ya kara da cewa “Abin takaici, duniyar da muke rayuwa a cikinta a yau ba haka lamarin yake ba, sakamakon rashin adalci da kuma bin salon siyasa mai harshen damo wajen mu’amala a duniya.

Ya kara da cewa “Duk wanda ke rayuwa a wannan duniyar tamu ya kamata ya sami dama daidai gwargwado.”

Pezeshkian ya sauka a filin sauka da tashin  jiragen sama na John F. Kennedy da ke birnin New York a daren Lahadi, inda ya samu tarba daga jami’an diflomasiyyar Iran da ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi wanda tuni ya isa birnin New York a daren Juma’a.

Kafin tafiyar tasa, ya bayyana fatansa na cewa zai zama muryar al’ummar Iran a taron Majalisar Dinkin Duniya da zai yi jawabi a wannan Talata.

A yayin zamansa na kwanaki 3 a birnin New York, an shirya shugaban na Iran zai gana da shugabannin kasashen duniya da dama, da jami’an wasu kasashen duniya, da kuma kafofin yada labarai na kasashen waje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments