Babban Darakatan Hukumar IAEA Ya Kai Ziyara Zuwa Zauren Baje Kolin Kayakin Da Iran Ta Samar Da Fasaharar Nukliya A Vienna

Rafael Grossi babban daractan hukumar makamashin nukliya ta Duniya (IAEA) ya ziyarci babban zauren baje kolin kayakin da gwamnatin kasar Iran ta samar tare da

Rafael Grossi babban daractan hukumar makamashin nukliya ta Duniya (IAEA) ya ziyarci babban zauren baje kolin kayakin da gwamnatin kasar Iran ta samar tare da amfani da fasahar Nukliya, a gefen taron gwamnonin hukumar karo na 68th a birnin Vienna babban birnin Austria.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya ce, wannan yana zuwa ne a dai dai lokacinda kasar Iran take cika shekaru 50 a duniya da fara aiki da fasahar Nukliya.

Shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran Muhammad Islami ya na tare da babban daraktan a lokacinda ya ziyarci wurin baje kolin kayakin ci gaban da kasar Iran ta samu tare da amfani da fasahar Nukliya a baya bayan nan.

Labarin ya kara da cewa kayakin da Iran ta samar tare da amfani da fasahar Nucliya dai na bangaririn fasahar Nukliya 4 ne, wato bangaren samar da wutan lantarki, na’urar bincike, makamashin Nukliya, da kuma abinda ake kira ‘Radiation’.

Muhammad Islami dai yana birnin Vienna tun ranar litinin don halattan babban taron hukumar karo na 68th sannan ya gabata da jawabi a taron.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments