Shugaban Kasar Iran Yace: Amfani Da Na’urorin Sadarwa Don Cutar Da Mutane Aikin Ta’addanci Ne

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa amfani da kayakin sadarwa wanda mutane fararen hula suke amfani da su don cutar da su aikin

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa amfani da kayakin sadarwa wanda mutane fararen hula suke amfani da su don cutar da su aikin ta’addancin ce kuma abin kunya ne ga Amurka da kasashen yamma wadanda suke tallafawa HKI ta yi hakan.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Laraba, bayan da ya sami labarin fashe-fashen kayakin sadarwa wanda ake kira Pager ya auku a kasar Lebanon a ranar Talatan da ta gabata, wanda yayi sanadiyyar shadar mutane 12 a yayinda wasu kimani 3000 suka ji rauni.

Shugaban ya kara da cewa abinda ya faru a kasar Lebanon ya nuna cewa kasashen yamma musamman Amurka ba sa son zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya. Da suna so, da basu taimakawa HKI ta cutar da fararen huka masu yawa kamar haka ba.

A na shi bangaren ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa wannan shi ne sabin ayyulan ta’addanci na HKI kan mutanen kasar Lebanon, sannan ya kara da cewa tuna an aika da tawagar likitoci da jami’an jinya dauke da magunguna zuwa kasar Lebanon don tallafawa wadanda suka ji rauni sanadiyyar fashe-fashen na Pager.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments