Iran Ta la’anci Kisan Kiyashin Da Isra’ila Ke Ci Gaba Da Aikatawa A Gaza

Iran, ta yi allawadai da da kisan kiyashin da Isra’ila ke ci gaba da aikatawa kan al’ummar Falasdinu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Nasser Kanaani,

Iran, ta yi allawadai da da kisan kiyashin da Isra’ila ke ci gaba da aikatawa kan al’ummar Falasdinu.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Nasser Kanaani, ya yi tir da Isra’ila kan kisan gillar da take ci gaba da yi wa Falasdinawa, yana mai cewa wadannan laifukan yaki sun bata sunan kasashen yammacin duniya da ke ikirarin kare hakkin bil’adama.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Kanaani ya mayar da martani kan harin jiragen yakin Isra’ila da ya yi sanadin rayukan Falasdinawa biyu a birnin Rafah da ke kudancin Gaza a safiyar wannan rana.

Laifukan yaki da yahudawan sahyoniyawan suke yi a Falastinu ya wulakanta masu rajin kare hakkin bil’adama na karya a kasashen yammacin duniya.

Kalaman nasa dai na nuni da irin sukar da gwamnatin Tehran ta dade tana yi wa kasashen yammacin turai kan goyon bayan da suke baiwa Isra’ila, yana mai zarginsu da rufe ido kan laifukan yaki da Isra’ila ke aikatawa wadanda suka sabawa dokokin kasa da kasa.

Alkalumman baya-bayan nan sun nuna cewa Falasdinawa sama da 41,206 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila tun ranar 7 ga watan Oktoba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments