Wani jami’in hukumar abinci ta duniya ya bayyana cewa kalmomi kawai ba za su iya bayyana irin mummunan halin da mutanen Gaza suke ciki ba saboda hana shigo da abinci Gaza wanda gwamnatin HKI take yi.
Tashar talabijan tan Presstva nan Tehran ta nakalto Micheal Fakhir dan rahoto na musamman na MDD dangane da abinci yana fadar haka a shafinsa na X, a cikin wasu rubuce rubucen da ya dora a sahfin nasa.
Rahoton ya kara da cewa bayan fara yaki a ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata, kimani watanni 11 da suka gabata ke nan, sojojin HKI sun kara tsuke hanyoyin shigo da abinci cikin Gaza, kari a kan takunkuman da ta dorawa yankin tun shekara ta 2007.
Saboda irin wannan mummunan halin da mutane kimani miliyon 2.2 na gaza suke ciki ne ya sa, hukumar abinci ta duniya (FAO) ta yi gargadin cewa hana shigawar abinci da magunguna kwatakwata a cikin gaza, ya sanya Falasdinawa tsakanin mutuwa da makaman HKI ko kuma saboda yuwan da cututtuka.