Paparoma Francis Ya Ce Zaben Kasar Amurka Zaben Mai Muni Da Wanda Ya Fi Muni ne

Shugaban darikar kiristoci ta catholica na duniya Paparoma Francis, ya bayyana cewa zaben shugaban kasar Amurka tsakanin yan takara biyu, wato Trump da Haris, zaben

Shugaban darikar kiristoci ta catholica na duniya Paparoma Francis, ya bayyana cewa zaben shugaban kasar Amurka tsakanin yan takara biyu, wato Trump da Haris, zaben mai muni da mafi muni ne.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto paparoma Francis ya na fadar haka a Vatican. Ya kuma kara da cewa korar yan gudun hijira da kuma zubar da ciki wanda yake dai dai da kashe rai,  duk basu da kyau.

Paparoman ya bayyana haka ne bayan ya dawo daga rangadin kwanaki 12 zuwa wasu kasashen Asiya, kuma an yi masa tambayoyi dangane da zaben Amurka a lokacin rangadin amma ya ki bada amsa.

Paparoma dan shekara 87 yana jagorantar darikar kiristoci mafi girma a duniya. Sannan a Amurka kadai yana da mabiya kimani miliyon 52. Kuma a cikin wannan adadin masu zabi kiamani kashi 20% na manyan mutane mutane wadanda suka cancanci kada kukri’a a Amurka ne.

Za’a gudanar da zaben shugaban kasa a Amurka ne, a ranar 5 ga watan Nuwamba na wannan shekara ta 2024, tsakanin tsohon shugaban kasar Amurka Donal Trump da kuma mataimakin shugaban kasa mai ci Kamala Haris.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments