Aragchi: Dole Ne Kasashen Yamma Su Sauya Halinsu Na Dorawa Kasashe Takunkuman Tattalin Arziki

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa dole ne kasashen yamma su dawo daga rakiyar dorawan kasashe takunkuman tattalin arziki don bai

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa dole ne kasashen yamma su dawo daga rakiyar dorawan kasashe takunkuman tattalin arziki don bai da wani amfani.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aragchi yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa takunkuman tattalin arzikin a kan wata kasa alamace ta yaki da kasar, kuma ya zuwa yanzu takunkuman tattalin arzikin kasashen yamma sun kasa dakatar da Iran daga inda ta sa a gaba.

Don  haka ministan yace: yamakata kasashen yamma su sake lale, saboda ba wani takunkumin da zata hana kasar Iran yin abinda taga ya dace da ita.

Kafin haka dai a makon da ya gabata ne kasashen turai 3, Burtaniya, Jamus da Faransa suka dorawa kamfanin zirga zirgan jiragen sama na kasar Iran wato ‘IranAIr’ takunkuman tattalin arziki tare da zargin cewa Iran tana katsalanda a yankin Ukraine, kuma tana tallafawa kasar Rasha da makamai masu linzami samfurin Balistic.

Haka ma, hukumar baitul malin Amurka da ce dorawa daddaikun mutane 10 takunkuman tattalin arziki da kuma wasu kamfanoni 9 wadanda suke kasar Rasha da kuma Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments