Babban Sakataren MDD Ya Yi Allah Wadai Da Kai Harin Kan ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinawa

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah-wadai da harin da aka kai kan wata makaranta da ke dauke da ‘yan gudun hijira a Nuseirat

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah-wadai da harin da aka kai kan wata makaranta da ke dauke da ‘yan gudun hijira a Nuseirat

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah wadai da luguden wutan da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan wata makaranta da ke dauke da ‘yan gudun hijira a sansanin Nuseirat da ke tsakiyar Zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadin shahadan Falasdinawa 18 da suka hada da kananan yara da mata da kuma ma’aikatan Hukumar Ba Da Agaji ga ‘Yan Gudun hijiranFalasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya ta UNRWA guda shida.

Har ila yau babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guterres ya sake sabunta kiransa na tsagaita bude wuta cikin gaggawa, wata sanarwa da kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya fitar ya fitar ta ce: Ba za a amince da ci gaba da rashin samar da ingantaccen kariya ga fararen hula a Gaza ba.

Sanarwar ta ce luguden wuta da sojojin mamaya suke yi kan fararen hula na baya-bayan nan ya janyo karuwar adadin ma’aikatan Hukumar UNRWA da suka mutu a Gaza zuwa 220, tare da jaddada bukatar gudanar da bincike mai zaman kansa kuma na gaskiya kan lamarin don tabbatar da daukar mataki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments