Na’urorin daukar hutunan bidiyo kusa da karamin ofishin jakadancin HKI a birnin Boston na kasar Amurka sun dauki hotunan wani mutum wanda har yanzun ba a san ko shi waye ne ba, yana kona kansa mai yuwa saboda abinda yake faruwa a zirin gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto tashar talabijin ta ‘ NBC10 Boston’ na bada wannan labarin a jiya Alhamis. Ta kuma kara da cewa al-amarin ya auku ne da misalign karfe 8:15 na yamma a kusa da wani hotel mai suna’ Four Seasons hotel’ wanda yake daba da karamin ofishin jakadancin HKI a birnin.
Jami’an tsaro sun zo sun dauki mutumin sun kai shi wani asbiti, amma babu labarin halin da yake ciki. Hakama sun dauki abubuwan gwaje – gwaje da suke bukata don ci gaba da bincike. Sannan sun gudanar da bincike a yankunan da ke kewaye da wurin don tabbatar da tsaro da zaman lafiyar mutane a yankin.
Wadanda suka ganewa idanunsu sun bayyana al-amarin a matsayin mai ban tsaro. Kafin haka dai wani sojan Amurka mai suna Aaron Bushnell ya kona kansa a gaban ofishin jakadancin HKI a birnin Washington a cikin watan Fabrairun shekata ta 2024, inda a fili ya bayyana cewa yana kona kansa ne saboda abinda yake faruwa a Gaza, kuma ya bayyana kubutarsa daga aikata abinda gwamnatin kasar Amurka da sojojin HKI suke aikatawa a Gaza na kissan kiyashi ga al-ummar Falasdinu.