Donald Trump Yace Zai Yi Maganin Kasashen Da Suke Kauracewa Dalar Amurka A Duniya

Tsoron shugaban kasar Amurka kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Republican ya tabbatar da cewa kasashen da dama a duniya suna kauracewa dalar Amurka

Tsoron shugaban kasar Amurka kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Republican ya tabbatar da cewa kasashen da dama a duniya suna kauracewa dalar Amurka a matsayin kudi na harkokin kasuwanci a duk fadin duniya kuma ya ce zai yi maganinsu idan an sake zabenasa a matsayin shugaban kasar Amurka a zaben watan nuwamba na wannan shekarar.

Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto Donald Trump yana fadar haka a taron yakin neman zamensa a jihar Wisconsin a kasar Amurka.

Trump ya kara da cewa idan an sake sabensa a matsayin shugaban kasar Amurka zai yi aiki don tabbatar da cewa dalar Amurka ce kudin ajiyar dukiyoyi a duniya da kuma musayar kudade a kasuwanci.

Trump yace zai yi amfani da takunkuman tattalin arziki mafi muni a kan kasashen da suke amfani da wasu hanyoyi don harkokin kasuwanci a duniya banda dalar Amurka.

Kafin haka dai kasashen Iran, China da Rasha sun fara shirin kauracewa dalar Amurka saboda gwamnatin Amurka ta maida dalar a matsayin makami don yakar kasashen da basa dasawa da ita.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments