Guinea Bissau : Ba Zan Nemi Takara Domin Yin Tazarce Ba_Embalo

Shugaban Kasar Guinea Bissau Umaro Cissoko Embalo ya sanar da cewa ba zai nemi takara domin yin tazarce ba a zaben da za a yi

Shugaban Kasar Guinea Bissau Umaro Cissoko Embalo ya sanar da cewa ba zai nemi takara domin yin tazarce ba a zaben da za a yi a kasar a cikin watan Nuwamba.

A watan Janairun 2020 ne Ambalo mai shekara 51 ya lashe zaben shugaban kasar, inda ya maye gurbin tsohon shugaban kasa Jose Mario Vaz.

Embalo, wanda yake da damar sake tsayawa takara, ya yanke shawarar kin neman tazarcen ne, wanda ake tunanin zai bude wata kofar zafafa siyasar kasar.

Shugaban ya bayyana hakan hakan ne a karshen taron majalisar ministocin kasar, inda ya ce matarsa ce ta ba shi shawarar janyewa daga neman takarar.

Sai dai bai bayyana wanda zai maye gurbinsa ba.

Ambalo wanda tsohon janar na sojin kasar ne Sau biyu yana tsallake yunkurin hambarar da gwamnatinsa.

Na karshe shi ne wanda akayi a watan Disamban 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments