Zulum: Ambaliyar Ruwan Maiduguri Ta Shafi Mutane Sama Da Miliyan Daya

Gwamnatin Jihar Borno, ta bayyana cewar mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu anguwannin birnin Maiduguri ta shafi kimanin mutane miliyan daya tare da lalata

Gwamnatin Jihar Borno, ta bayyana cewar mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu anguwannin birnin Maiduguri ta shafi kimanin mutane miliyan daya tare da lalata dukiyoyin miliyoyin kudi.

Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum ne, ya bayyana hakan ga manema labarai, yayin da yake raba kudi da abinci ga mutane da suka nemi mafaka a sansanin ‘yan gudun hijirar Bakassi da ke Maiduguri a ranar Laraba.

Zulum, ya ce an kafa kwamitin agajin gaggawa domin dakile barkewar cututtuka masu nasaba da ambaliyar ruwa a Maiduguri.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), ta tabbatar da cewa sama da mutane 200,000 ne suka rasa mahallansu sakamakon ambaliyar.

Kawo yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba, sai dai NEMA ta ce wasu mutane ciki harda kananan yara sun bace.

Wuraren da lamarin ya shafa sun hada da bababar Kasuwar Maiduguri Monday Merket, da fadar Shehun Borno, da babban asibitin koyarwa, da gidan gyran hali na New Prison.

Mazunan wadannan unguwanni sun ce har yanzu suna ci gaba da neman wasu ‘yan uwansu da suka bace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments