Ministocin Wajen Kasashen Larabawa Sun Bukaci Isra’ila Ta Fice Gaba Daya Daga Gaza

Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa, sun bukaci Isra’ila ta fice gaba daya daga zirin Gaza, ciki har da titin Philadelphi da kuma mashigar Rafah ta

Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa, sun bukaci Isra’ila ta fice gaba daya daga zirin Gaza, ciki har da titin Philadelphi da kuma mashigar Rafah ta bangaren Palastin.

An gabatar da bukatar ne a cikin wani kuduri da aka fitar bayan taro karo na 162 na kungiyar ministocin wajen kasashen Larabawa (AL) da aka gudanar a birnin Alkahira na kasar Masar.

Ministocin sun yi watsi da shirin Isra’ila na ci gaba da mamaye yankin zirin Gaza.

Al’ummomin kasashen larabawa da dama dai suna ganin cewa gwamnatocinsu sun gaza dangane da daukar kwararan matakan da suka dace wajen fuskantar kisan kiyashin da Isra’ila ke yia  yankin zirin Gaza.

Baya ga jami’ai daga Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan shi ma ya halarci taron, wanda ya kasance karo na farko da babban jami’in diflomasiyyar Turkiyya ya halarci taron ministocin (AL) cikin shekaru 13 da suka gabata.

Duk da ayyukan kisan kare dangi da Isra’ila take aikatawa, babu ko daya daga cikin kasashen larabawa da suka da alaka da Isra’ila da suka yanke wannan alaka, bil hasali ma suna ci gaba da gudanar da harkoki na diflomasiyya da mu’amalloli na kasuwanci.

Kasashen Masar, UAE, Jordan, Morocco da Bahrain ne dai suke da alaka ta diflomasiyya kaitsaye da Isra’ila, kuma ayyukan yaki na Isra’ila basu sanya wadannan kasashe sun yanke alakarsu da Isra’ila ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments