Isra’ila Ta Ce Akwai Yiyuwar Sojojinta Ne Suka Harbe Matashiyar Nan Yar Asalin Turkiyya

Rundunar sojin Isra’ila ta ce akwai yiyuwar sojojinta ne suka harbe matashiya nan yar asalin kasar Turkiyya a wata zanga-zanga a gabar yamma da kogin

Rundunar sojin Isra’ila ta ce akwai yiyuwar sojojinta ne suka harbe matashiya nan yar asalin kasar Turkiyya a wata zanga-zanga a gabar yamma da kogin Jordan da ta mamaye a makon da ya gabata.

Aysenur Ezgi Eygi, mai shekaru 26, tana zanga-zanga ne a garin Beita, kusa da Nablus, don nuna adawa da fadada matsugunan Yahudawa a ranar 6 ga Satumba.

Shaidu da jami’an Falasdinawa sun ce sojojin Isra’ila ne suka harbe ta, lamarin da ya sa rundunar sojin Isra’ila ta gudanar da bincike.

Sakamakon binciken da suka fitar a ranar Talata ya kammala da cewa “akwai da yuwuwar rundunar IDF ta harbe ta ne cikin kuskure.

A cikin sanarwar “Rundunar ta IDF ta bayyana matukar bakin cikinta game da rasuwar Aysenur Ezgi Eygi.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments