Jagora Ya Ce Makiya Suna Gwada Kansu A Matsayin Masu Karfi  Domin Cimma Munanan Manufofinsu

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Fankaman karfi shi ne tushen yakin kwakwalwa na makiya a kan al’ummu A yayin ganawarsa da masu

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Fankaman karfi shi ne tushen yakin kwakwalwa na makiya a kan al’ummu

A yayin ganawarsa da masu shirya taron girmama shahidan lardin Kohgiluyeh da Boyer Ahmad da ke shiyar kudu maso yammacin kasar Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Fankaman karfi shi ne tushen yakin kwakwalwa da makiya ke yi a kan al’ummu.

Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya kara da cewa: Lardin Boyer Ahmad, lardi ne mai dauke da tarihin sadaukarwa da jihadi a matakin yakin kare kai mai alfarma, kuma jagoran ya tabo tushen dalilin gudanar da yakin kwakwalwa da makiya suke yi ga al’ummu, da suka hada da fankama girmansu da cusa jin tsoronsu.

Jagoran yana mai jaddada cewa: Daya daga cikin gagarumar nasarori masu girma da Imam Khomeini {yardan Allah ya tabata a gare shi} shi  ne kawar da tsoron manya kasashe masu girman kai daga zukatan al’umma da dasa ruhin aminci da yarda a zukatansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments