Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Kokarin ‘Yan Sahayoniyya Shi Ne Juyar Da Gaskiya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Yunkurin ‘yan sahayoniyya na danganta duk wani lamari da Iran neman gujewa gaskiya ce A taron

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Yunkurin ‘yan sahayoniyya na danganta duk wani lamari da Iran neman gujewa gaskiya ce

A taron manema labarai da ya gudanar; Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa: Yunkurin da yahudawan sahayoniyya suke yi na alakanta duk wani lamari mummuna da Iran, kokari ne na tserewa daga hakika, wanda ke nuni da cewa wannan gwamnati wata cutar kansa ce kuma cikakken sharri a yankin.

Kan’ani ya yi nuni da cewa: Fushin al’umma kan Yahudawan Sahayoniyya saboda munanan laifukan yaki da take aikatawa a Gaza da kuma na baya-bayan nan a yankunan gabar yammacin kogin Jordan, ya ce, ko shakka babu suna daukar batun tallafa wa Falasdinu a matsayin halin kwarai da jin kai na dan Adamtaka, amma yunkurin da ‘yan sahayoniyya suke yi na alakanta duk wani mummunan lamari da Iran tserewa ne daga gaskiya.

Kan’ani ya kara da cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya sun bude kofofin wuta na kona kansu ta hanyar ci gaba da rura rikici a Gaza tare da dagewa kan cewa ba za su amince da tsagaita bude wuta ba, kuma wannan matakin babu abin da haifar musu ban da karin hasara.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya ce: Wani babban jami’in yahudawan sahayoniyya ya yarda cewa wannan gwamnati ta ‘yan mamaya ta fi kusa da shan kashi fiye da samun nasara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments